Hukuncin daurin rai da rai kan Beate Zschaepe
July 11, 2018Bayan an kwashe kimanin shekaru biyar ana zaman shari'a, a yau Laraba aka yanke hukunci daurin rai da rai a shari'ar da ake wa wasu 'ya'yan kungiyar ta'adda masu kyamar baki a Jamus. A fadin Jamus gaba daya an kasa kunne a ji sakamakon wannan hukuncin na masu ra'ayin kyamar bakin da suka aikata kisan kai kan baki guda 9 tsawon shekara biyar.
Farkon wanda lamirin na kisan mai ban al'ajabi ya rutsa da shi ya rasu a shekarar 2000 sannan na karshe a shekarar 2006. Mutum tara ne, takwas 'yan asalin kasar Turkiyya daya kuma daga kasar Girika. Da bindiga iri daya aka harbe su har lahira. Masu bincike sun yi zaton wadanda suka yi kisan 'yan fataucin miyagun kwayoyi ne, ba su taba tsammanin kisan na da alaka da kyamar baki ba. Wannan batun ya yi matukar daukar hankali a nan Jamus, saboda alakarsa da kyamar baki.