Jamus: Matsayi kan motocin Diesel
February 27, 2018Wata babbar kotu da ke birnin Leipzig a Jamus za ta yanke hukunci kan yiwuwar haramta zirga-zirga da motoci masu amfani da man Diesel, a manyan biranen kasar saboda dalilai na lafiya da na muhalli. A ranar Alhamis na makon jiya ne, kotun ta share sa'o'i hudu tana nazari kan wannan lamari, inda ake sa ran da ranar Talata za ta yanke hukunci kan batun.
Kotun dai ta yi nazarin hukunce-hukncen farko ne da wasu kananan kotunan biranen Stuttgart da Dusseldorf suka yanke kan manyan motocin na safa. Yayin da kotun na Stuttgart ke ganin dacewar haramta amfani da motocin, ita kuwa kotun Dusseldorf cewa ta yi akwai bukatar dogon nazari.
Kamfanonin kera motoci a nan Jamus dai sun fara fuskantar rudani kan motoci masu amfani da man na Diesel din ne a shekara ta 2015, bayan wani zargin da aka yi wa kamfanin Volkswagen, kan wasu matakan da suka danganci hayakin da motocin ke fitarwa.