1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Putin: Rasha ba ta bukatar yaki a Turai

Abdullahi Tanko Bala
February 15, 2022

Rasha ta fara janye sojojinta daga iyakar Ukraine. Sai dai har yanzu ana cigaba da tattaunawar diflomasiya domin kwantar da rikicin.

https://p.dw.com/p/4743s
Rasha| Olaf Scholz ya gana da Vladimir Putin a birnin Mocow
Hoto: Mikhail Klimentyev/Sputnik/dpa/picture alliance

Rasha da kasashen yammacin Turai dai sun sami rarrabuwar kawuna akan batutuwa da dama ciki har da batun fadada kungiyar tsaro ta NATO.

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya gana da shugaban Rasha Vladimir Putin a birnin Moscow inda batun Ukraine ya kasance kan gaba a jadawalin tattaunawa. Scholz ya baiyana fara janye sojojin Rasha daga iyakar Ukraine da cewa wata alama ce mai armashi.

Bayan ganawa da shugaban Rasha Vladimior Putin, Scholz yace hakkin mu ne mu samo hanyoyi na lumana da fahimtar juna don kawo karshen wannan rikici ba tare da tauye hakkin kowa ba yana mai cewa wasu muradun da Rasha ta gabatar abin dubawa ne.

A waje guda dai Shugaban na Rasha Vladimir Putin yace kasarsa ba ta bukatar yaki bayan kasashen yamma sun zarge shi da jibge sojoji a kusa da iyaka da kasar Ukraine da cewa shiri ne na mamaye kasar.

Putin yace a shirye suke don cigaba da tattaunawa kan tsaro da sauran batutuwa.