1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Jarirai 29 da aka kwashe daga Al-Shifa sun isa Masarrafah

November 20, 2023

Hukumomin kiyon lafiya na Masar sun tabbatar da isowar jarirai 29 bakwaini da aka kwashe daga asibitin al-Shifa na Gaza i zuwa birnin Rafah da ke zama kofa daya tilo da ke sada yankin Falasdinu da duniya.

https://p.dw.com/p/4ZD6k
Gazastreifen, Rafah | Evakuierte Neugeborene aus dem Al-Shifa Krankenhaus
Hoto: Abed Rahim Khatib/dpa/picture alliance

An kwashe jariran 29 daga asibitin Al-Shifa wanda hukumar lafiya ta duniya WHO/OMS ta bayyana a matsayin ''tarkon mutuwa'' a ranar Lahadi (19.11.2023) i zuwa asibitin Emirates da ke birnin Rafah mai raba iyaka da Kundancin zirin Gaza.

Karin bayani: WHO na neman a kwashe mutane daga asibitin al-Shifa na Gaza

A lokacin isarsu Masar, tashar talabijin din kasar Al-Qahera News ta ruwaito cewar jariran sun isa salim-alim a cikin kwalabe da aka hade da na'urorin kula da lafiya sannan kuma za a daukin nauyinsu baki daya.

Karin bayani: Daruruwan marasa lafiya da dubban mutanen da suka fake a asibitin Gaza na cikin tashin hankali sakamakon fadan sojin Isra'ila da Hamas a harabarsa

Hukumar lafiya ta duniya WHO wacce ta sa ido a lokacin kwashe jariran 29 ta ce 11 daga cikinsu na fama da matsananciyar rashin lafiya, sannan kuma babu ko da guda daga cikinsu da ya samu rakkiyar iyayensa yayin da kuma biyu suka mutu kafin a kwashesu.