1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jigilar jirage ta soma tsayawa a Afirka

March 21, 2020

Kamfanonin jiragen sama na nahiyar Afirka da ke zuwa manyan kasashen duniya, sun sanar da soke harkokinsu a jiya Juma'a sakamakon barazanar cutar coronavirus.

https://p.dw.com/p/3ZpJb
Südafrika South African Airlines Flugzeuge am Flughafen Johannesburg
Hoto: picture-alliance/imageBROKER/M. Bail

Kamfanin jiragen kasar Afirka ta Kudu na daga cikin kamfanonin da suka sanar da daukar wannan matakin na dakatar da zirga-zirga.

Haka nan kamfanin Ethiopian Airlines wanda ya fi kowanne karfi a harkokin sufurin sama a nahiyar, ya sanar da soke jigila zuwa kasashe 30.

Dama dai an dauki lokaci ana zargin kamfanin na Ethiopian Airlines, da sanya nahiyar Afirka cikin hadarin wannan cuta, saboda ci gaba da ya yi da jigila zuwa kasashen da cutar ta yi kamari a cikin su, musamman ma kasar China inda wannan cuta ta samo asali.

A yanzu dai kasar Afirka ta Kudu ce ke kan gaba a Afirkar da yawan mutum 202 da suka kamu da cutar sarkewar numfashin ta COVID-19.