Wagner ya yi karin haske a kan kisan mayakansa a Mali
October 9, 2024Talla
Kamfanin sojojin hayar Rasha wato Wagner, ya ce ya gano gawarwakin mayakansa da aka kashe a wata arangama da 'yan tawayen Mali cikin watan Yulin da ya gabata.
Kamfanin na Wagner ya tabbatar da asarar dumbin sojoji cikin watan Yulin, amma kuma bai bayar da alkaluma ba.
Kasar Mali wadda sojoji suka kifar da gwamnatin dimukuradiyya yau shekaru uku, ya kwashe shekaru yana fama da matsalar ta'adddanci daga mayaka masu tsaurin ra'ayi.
Asarar sojojin na Wagner cikin makonnin da suka gabata dai, na nuna girman kalubalen da ke gaban kamfanin sojojin na hayar Rasha da ke aiki da gwamnatocin soja na kasashen Sahel wadanda ke kokarin yakar ta'addanci.