Kamfanonin kera jirage sun sallami ma'aikata
April 29, 2020Kamfanin kera jiragen sama na Boeing, ya ce zai rage ma'aikata da za su kai kashi 10%, bayan ya sanar da asarar dala miliyan 641 a watanni uku na farkon wannan shekara, saboda illar da Korona ta yi masa.
Haka nan zai dakatar da wasu daga cikin manyan jiragen jigilar fasinjoji da yake kerawa da suka hada da samfurin 787 da kuma 777
A baya a daidai wannan lokacin kamfanin na Boeing na sanar da riba ce ta sama da dala biliyan biyu.
A bayyana take dai harkokin surufin sama, za su kwashe shekaru kafin sake komawa yanda aka saba, don haka ne shugaban kamfanin, David Calhoun, ke cewa tilas ne a shirya wa yanayin.
Dama dai kamfanin na da ma'aikata dubu 160 ne, abin da a yanzu zai shafi mutum dubu 16 ke nan.
Shi ma kamfanin kera jirage na Airbus da ke nan Turai, ya sanar da asarar euro miliyan 481 kwatankwacin dala miliyan 151, tare da sallamar dubban ma'aikata.