Ranar farko ta Trump a kan mulki
January 26, 2017Talla
Soke yarjejeniyar cinikayyar ta TTP da Donald Trump ya yi ba ta zo da mamaki ba, domin dama ta na daga cikin alkawuran da ya yi a lokacin yakin neman zabe.
Ita dai yarjejeniyar ta TTP wadda kasashe 12 suka sanya hannu ta na harkokin cinikayya da suka tasamma kashi 40 cikin dari na tattalin arzikin duniya.