Takunkumin Turai kan man fetur din Rasha
February 3, 2023Talla
A lokacin da yake bayani a birnin Moscow, Dmitri Peskov da ke zama kakakin fadar shugaban Rasha ya tabbatar da cewa kasarsa na daukar matakan kare tattalin arzikinta daga barazanar takunkumin.
A ranar lahadi mai zuwa ne wannan takunkumin zai fara aiki, kuma sakatariyar zartarwa ta Kungiyar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen ta nuna cewa wannan takunkumi zai rage wa Rasha samun zunzurutun kudi da ya kai miliyon 160 na yuro a duk rana.
Sai dai masana kasuwacin man fetur sun ce takunkumin na Turai na iya haifar da hauhawar farashin man fetur a Turai. Amma wasu kasashe sun fara karkata ga Amirka da kuma Saudiyya don cike gibin da suke samu a fannin man fetur da sauran makamashi.