Kenya: Gobara ta rutsa da mutane da dama
February 2, 2024Hadin gwiwar jami'an tsaro da na kiwon lafiya sun garzaya da wadanda suka samu munanan raunuka asibiti kamar yadda kwamandan 'yan sandan yankin Adamson Bungei ya sanar, duk da cewa alkaluman hukumar Red Cross ta Kenya na cewa adadin wadanda suka jikkata ko lamarin ya rutsa da su ka iya zarta hakan.
Mai magana da yawun gwamnatin Kenya, Isaac Mwaura, ya ce lamarin ya afku ne sakamakon fashewar wani bututun iskar gas da har yanzu ake ci gaba da gudanar da bincike kan musabbabin afkuwar gobarar, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na X.
Wani dan jaridar kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya shaida cewa har zuwa karfe 6:30 na safe agogon Kenya, jami'an hukumar kashe gobara na ta kokarin shawo kan lamarin.
Wasu hotunan bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta sun nuna yadda hayaki ya turnuke sararin samaniyar babban birnin na Nairobi.