Kenya: Kammala taron koli na tsakanin Jamus da Afirka
February 10, 2017Taron kolin na kwanaki biyu kan tattalin arziki da cinikayya karo na biyu a tarihi tsakanin Jamus da kasashen na nahiyar Afirka, na da burin kyautata huldar kasuwanci tsakanin sassa guda biyu. Kuma ministan raya kasashe masu tasowa na Jamus Gerd Müller bisa ga dukkan alamu na da sha'awar ganin an samu karin jari daga Jamus zuwa nahiyar Afirka. Ministan ya ce Afirka na bukatar masu zuba jari da yawan gaske da za su kirkiro da guraben aikin yi musamman ga matasan nahiyar da dalilai na zaman kashe wando ke sa su neman gwada sa'arsu a wata nahiya ta kowace hanya.
Mahimmancin karin zuba jari a Afirka
"Yawan matasa marasa aikin yi kimanin kashi 50 cikin 100 ba abu ne mai kyau ba ga makomar kasa. Kowane matashi na bukatar ilimi da kuma aiki. Wannan shi ne babban kalubale ga wannan gwamnati tan Kenya a cikin shekaru biyar masu zuwa nan gaba. Za mu kasance babbar abokiyar hulda ga kasar Kenya."
Matakin zuba jari a Afirka na sahun gaba a shirin kasar na kulla sabon hadin kai da Afirka da ministan ya kaddanmar mai taken Marshall Plan ga Afirka da ke da burin farfado da tattalin Afirka. Sai dai a Berlin fadar Gwamnatin ta Jamus ana saka ayar tambaya ga shirin na Marshall Plan kasancewa ministan ba shi da hurumin aiwatar da akasarin matakan da ke kunshe cikin shirin.
Kawo yanzu dai harkokin tattalin arziki da Jamus ke gudanarwa a Kenya ba su da yawa. Don ganin abubuwa sun sauya ministar harkokin wajen Kenya Amina Mohamed ta yi kira ga 'yan kasuwar Jamus da su shiga cikin bangarorin kasuwancin kasar ta Kenya.
Neman zuba jari na kamfanonin Jamus a kasashen Afirka
"Ina son in mika goron gayyata ga kamfanoni da kuma 'yan kasuwar Jamus da su shigo cikin harkokin tattalin arzikin Kenya musamman a fannonin fasahar sadarwa da masana'antu da aikin gona da tono ma'adanan karkashin kasa da sufuri da kuma samar da makamashi. Su na iya yin haka ta hanyar hadin kai da kamfanonin Afirka ko kuma ma'aikataun gwamnati."
Sai dai matsalar cin hanci da rashawa na daga cikin matsalolin da ke hana ruwan guda. A kan haka ne ministan raya kasa na Jamus Gerd Müller ya yi kira ga Afirka da ta kirkiro da kyaukyawan yanayin zuba jari ta hanyar yaki da cin hanci da rashawa. Yana mai cewa dole ne a ga ci-gaba a yaki da rashawa tare kuma da kafa dokokin da za su kare kamfanoni.