Kenya: Shekaru 60 da samun mulkin kai
December 12, 2023A yayinda ake bukuwan samun 'yancin kai na shekaru 60 a birane da da sauran ma'aikatun gwamnati, ba duka 'yan kasar ba ne ke murnanr samun 'yancin kan, inda wasu mutane ba sa jin dadin bikin ko kadan. Domin kuwa ta yi musu tsada, ba za su iya cin abinci sau uku a rana ba, watakila ma ba abinci sau biyu a rana. A cewar Berline Ndolo, manajar shirye-shirye na kungiyar Wonesu, wata kungiyar da ke tallafa wa mutane a lardin Kisumu da ke yammacin Kenya, suna samar wa talakawa tallafin ilimi, ta ce ita Kanta ta rayau cikin tsananin talauci.
"Kuma zan ce wannan gungun jama'a na musamman ba za su iya jin farin ciki a ranar samun Jamhuriya ba. Dalilan kuwa, na daya, domin idan aka yi la'akari da tsadar rayuwa a halin yanzu ta yi musu tsada, ba za su iya cin abinci sau uku a rana ba, watakila ma ba za su iya samun abinci sau biyu a rana ba. Don haka za su maida hankali kan yadda za su iya ciyar da iyalansu da dan abin da suke da shi."
Wata babbar matsalar da kasar Kenya ta ke fama da ita dai ita ce bambancin kabila, domin idan ka tambayi mutane a Kenya game da wani lokaci mai ma'ana a tarihin kasarsu, to za su ce maka rikicin da ya biyo bayan zaben 2007, lokacin da dan karamin sakamakon zabe ya haifar da rikicin kabilanci, koyaushe yana tasowa a zukatan 'yan kasar. An kashe mutane kusan 1,500 tare da raba dubbai da muhallansu a wancan lokacin. Peter Muchiri wani ma'aikacin otel cewa yi wannan tashin hankali ya zama babban darasi ga ‘yan kasar baki daya.
"Mutane sun koyi darasi, sun koyi kaunar juna duk da bambancin kabila, saboda a lokacin an zubar da jini da yawa, kasar ta fada cikin rudani, don haka mutane sun koyi darasi da yawa daga wannan, domin yanzu babu wannan kabilanci. Rikici ko kabilanci, hakika ya ragu idan aka kwatanta da yadda yake a da."
Idan dai aka yi misali da shugaba William Rutto da ke mulkin kasar a yanzu, za a iya cewa batun kabilanci ya ragu, domin kuwa shi ya fito ne daga karamar kabila a kasar, kai ga wasu ma yakin neman zaben Rutto ya yi shi ne da sunan bambancin attajiarai da matalauta. James Shikwati shi ne wanda ya kafa cibiyar hada-hadar tattalin arziki da ke da nufin dinke yakunan kasar Kenya.
"Ya dora kamfen dinsa ga al'ummar Kenya cewa kada a dogara da kabilanci, don a yi nuni da cewa wannan kabilar, waccan kabilar. Ma'ana mutane kada su bari a yaudare su da sunan kabilanci. Irin wannan sako lokaci zuwa lokaci, ina tsammanin ya yi aiki mai kyau akan hakan."
Duk irin koma bayan rikicin kabilanci da raunin mulkin dimukuradiyya, kasar Kenya a yanzu za a kwatantata da wadanda suka samu ci gaba a Afirka, inda misali a fannin sufuri ta ke da jiragen kasa masu sauri, wanda kama daga tsakiyar Nairobi babban birnin kasar a minti 15 mutum zai isa babbar tashar jiragen saman kasar, haka kuma akwai jirgin kasa mai sauri da ke zuwa har birnin Mombas da ke babbar tashar jiragen ruwa. Wannan da sauransu na iya nuna ci gaba da kasar ta gabashin Afirka ta samu bayan 'yancin kai shekaru 60 da suka gabata.