Khashoggi: Turkiyya za ta yi bincike
October 15, 2018Talla
A wannan Litinin ne ake sa ran masu bincike a Turkiyya, za su gudanar da aikinsu a ofishin jakadancin Saudiyya da ke birnin Istambul, a karon farko bayan bacewar dan jaridar nan Jamal Khashoggi.
Hakan na zuwa ne bayan wata tattaunawar da ta wakana ta wayar tarho tsakanin shugaban Turkiyya Racep Tayip Erdogan da kuma Yerima mai jiran gado na Saudiyya, Mohammad bin Salman.
Kimanin makonni biyu ke nan da bacewar Mr. Khashoggi, da ya shiga ofishin jakadancin Saudiyyar da ke Istambul, inda zargin kisan shi ke kan mahukuntan Saudiyya.
Tuni ma dai Amirka da ta yi bazaranr daukar mataki mai tsauri, ta shirya aike wa da ministan harkokin wajenta Mike Pompeo, zuwa Saudiyyar a kan wannan batu.