Kiev da Mosko sun cimma yarjejeniya
April 17, 2014Ministan harkokin wajen Rasha Sergei lavrov ya sanar cewa kasarsa ta cimma yarjejeniya tare da Ukraine da Amirka da Tarayyar Turai, wadda za ta rage zaman zullumin da ake yi a tsohuwar daular ta Sobiet. Daga cikin tanade-tanaden da wannan yarjejeniya da suka cimma, a tattaunawar da suka gudanar a birnin Geneva na kasar Switzerland ta yi, an bukaci duk kungiyoyin dake dauke da makamai a yankuna Ukraine su kwance dammarar su.
Sergei Lavrov ya bayyana cewa bangarori hudun da suka taru a birnin Geneva a wannan alhamis, wato Amirka, Turai, Ukraine da Rasha, za su yi aiki tare wajen ganin sun kaddamar da tattaunawar kasa domin kare hakkin jama'a.
Ya kuma bayyana cewa za a yi wa masu tada kayar bayan dake goyon baya rasha afuwa, musamman wadanda ke da hannu a bijirewar da aka yi wa gwamnatin Kiev sai dai banda wadanda suka aikata manyan laifuka.
Ita dai Rasha, ta na goyon bayan kiran da aka yi na cewa 'yan awaren Ukraine su ajiye makamansu, su kuma fita daga gine-ginen gwamnatin da suka kame, domin dama tun farko a wata hira da yayi da wani gidan talabijin Putin ya karyata zargin cewa mahukuntan Moskow na bayan tarzomar da magoya bayan rashar ke yi
Takaddama mafi tsauri tun bayan yakin cacar baka
"Wannan labarin banza ne, a yankin gabashin Ukraine babu dakarun Rasha, babu masu leken asiri, babu ma masu baiwa sojoji shawara. Al'ummomin yankin ne ke yin wannan rikicin. Hujjar ita ce ana ganin mutanen da suke yi, domin ba su boye fiskokinsu ba, wannan na fadama takwarori na na yamma, mutun ba zai bi ta kan mutanen yayi tattaunawa ba, su 'yan kasa ne kuma dole ne a tattauna da su"
Wannan lamari na Ukraine, shi ne takaddama mafi girma tsakanin gabas da yamma tun bayan yakin cacar baka. Kowane bangare dai ya zo da na sa bukatar, domin jami'an leken asirin Ukraine sun ce a makonni shidan da suka gabata, sun kama masu leken asirin Rasha, wadanda suke kyautata zaton sun zo ne su tada zaune tsaye a kasar amma Rasha ta karyata hakan, duk da hakikancewar da jami'an leken asirin Ukraine din suka yi na cewa wadanda suka tabbatar yankin Kirimiya ya fada hannun Rashar ne suke yankin na su a yanzu.
Tanade- tanaden sabuwar yarjejeniya
Wannan yarjejeniya dai za ta dakatar da takunkumin karya tattalin arzikin kasahen yamma suka yi niyyar kakabawa Rasha idan da ba a tashi da wani mataki na bai daya daga taron ba, wannan kuma zai dan sassauta yanayin tankiyar dake tsakanin mahukuntan Mosko da kasashen Turan da ke dogaro da ita wajen samun i makamashi.
Sakataren kula da harkokin wajen Amirka wanda shi ma kamar sauran takwarorinsa ya yi bayani bayan da aka kammala taron ya ce ba wannan taron ne kadai matakin da suka dauka na kashe wutan wannan rikicin ba.
"Mun kuma amince, kuma a tunani na wannan na daga cikin mahimman batutuwan da muka maida hankali a yau, dukkanmu na so mu dauki matakai masu kwari ba maganar fatar baka ba, matakai masu kwari wadanda za su taimaka wajen kashe wutan rikicin, shi ya sa muka ce kungiyar sanya ido ta musamman ta OSCE, wadda ke nan a kasa, wacce kuma aka riga aka amince da kudurinta, su taka rawa ta musamman wajen tallafa mahukuntan Ukraine da kananan alummomi wajen aiwatar da matakan kashe rikicin da aka dauka"
Kerry ya kuma kara da cewa Rasha ta ba da tabbacin cewa a shirye take ta fara janye dakarunta dake kan iyakar Ukraine idan dai hat Ukraine ta fara aiwatar da matakan da suka amince da su a taron kuma ita ma Amirka za ta rage takunkumin da ta kakabawa wasu mutane a kasarta idan ta ga Rashar da gaske take yi.
Mawallafiya: Pinado Abdu Waba
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe