Kokarin saka wa Koriya ta Arewa takunkumi
August 5, 2017Talla
Hakan na zuwa bayan sabbin gwaje-gwajen makamai masu linzamin da ke cin dogon zango da Koriya ta Arewar ta yi. Yanzu dai a shirye kasar ta ke don rarraba daftarin kudurin bukatar hakan ga dukkanin mabobin kwamitin sulhun Majlisar ta Dinkin Duniya wanda tuni kuwa alamu suka nuna samun amincewar kasar China. Da ma dai Amirka da China na shawartawa dangane da tsara daftarin kudurin gabanin wannan matakin da aka kai. Ana bukatar sahalewar kasashe tara daga cikin mambobin kwamitin na sulhu kafin wannan kuduri ya haye.