Koriya ta Arewa ta kada hantar kasashe
May 14, 2017Talla
Cikin daren da ya gabata ne dai Koriya ta Arewar ta sake gwajin makami mai linzamin, abin da ake cewa ya saba tsarin gwajin makamai na duniya.
Cikin wata sanarwar da White House ta Amirka ta fitar, shugaba Donald Trump ya yi kiran hanzarta kakabawa Koriya ta Arewa manyan takunkumai saboda yin gaban kai ba tare da damuwa da damuwar mutane ba.
Sanarwar ta kuma nuna mamakin yadda makamin ya sauka dab da kasar Japan.
Shi ma sabon shugaban Koriya ta Kudu Moon Jae In, ya nuna fargaba kan barazanar makamin da Koriya ta Arewar ta gwada wanda kuma ya kai shi ga kiran taron majalisar tsaro na gaggawa.