Koriya ta Arewa ta sake gwajin makami
May 22, 2017Jerin gwaje-gwajen makamai masu linzamin da Koriya ta arewar ke yi cikin makonni yanzu, na ci gaba da kada hantar manyan kasashen duniya.
Bayan gwajin makamin da Koriya ta arewa ta bayyana samun nasararsa a jiya Lahadi, kasar China a wannan Litinin ta yi kiran kasashen da su kwantar da hankali. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Hua Chunying shi ne ya yi kiran da safiyar yau.
Koriya ta arewa dai ta bijirewa dukkanin gargadin da Majalisar Dinkin Duniya da sauran kasashe suka yi mata kan gwaje-gwajen, tana mai cewa tana abin ta ne a matsayin matakai na kare kai.
Shi dai makamin ya yi tafiyar kilomita 500, kafin ya sauka a kojin Japan, kamar yadda sojojin kasar Koriya ta kudu suka tabbatar. Ko a makon da ya gabata ma dai sai da ta gwada wani makamin mai linzami. Ta kuma yi ikirari a da safiyar yau cewa a shirye ta ke ta kera daruruwan makamin da acewarta za su iya cimma sansanonin sojin Amirka da da ma take hari.