1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Koriya ta Arewa ta yi gwajin makami

Ramatu Garba Baba
September 15, 2017

Babban magatakarda na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi alla-wadai da gwajin makami mai linzami da Koriya ta Arewa ta yi a wannan Juma'ar.

https://p.dw.com/p/2k3vw
Südkorea Raketentest
Hoto: picture-alliance/NurPhoto/South Korea Defense Ministry

Antonio Guterres ya nemi gwamnatin Koriya ta Arewa da ta gaggauta dakatar da duk wani gwajin makami tare da mutunta dokokin da kwamitin tsaro na Majalisar ya gindaya kan wannan batu bayan kafaffen yada labarai sun yi ta wasta labarin harba rokar da Koriya ta Arewa ta yi a wannan juma'ar.

Shugaban Rasha Vladimir Putin da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron na daga cikin shugabanin kasashen duniya da suka nuna damuwarsu kan wannan gwajin inda suka amince a tsakaninsu da shirya zama gaba da gaba da Koriya don warware wannan matsalar da ke barazana ga zaman lafiyar al'umma, a na shi bangaren Mista Guterres ya ce za su tattauna kan gwaje-gwajen makaman da duk bangarorin da lamarin ya shafa a gefen taron Majalisar da zai gudana a mako mai zuwa.