1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Koriya ta Arewa za ta sake gwajin makamin nukiliya

Mouhamadou Awal Balarabe
September 4, 2017

Koriya ta Kudu ta bayyana cewar takwararta ta Arewa na shirin sabon gwajin makamin kare dangi shigen wanda ta yi a karshen mako, lamarin da ya sa ta dauki matakan kare kanta daga barazana.

https://p.dw.com/p/2jKEg
Norkorea Rakete
Hoto: Getty Images/KCNA

Dama dai Koriya ta Arewar ta fara shelar cewar ta yi nasara hada wani makeken bam da za a iya harba shi daga wannan nahiya zuwa wancan. Lamarin da ya kara tada hankalin kasashen da ba sa dasawa da Koriya ta Arewa. To sai dai kwana guda bayan da Arewan ta yi wannan gwajin, takwararta Kudu ma dai ta gwada nata makami a matsayin martani ga mahukuntan Pyongyang.

Südkorea gemeinsame Manöver mit USA Rakete Hyunmoo Missile II
Kasashen duniya na cigaba da sukar Koriya ta Arewa kan gwajin makami mai linzami Hoto: Reuters/8th United States Army

A daura da wannan, shugaban Amirka Donald Trump ya ci gaba da tada jiyoyin wuya inda ya sake barazanar sa kafar wando guda da takwaran aikinsa na Koriya ta Arewa Kim Jong-Un idan ya kuskura ya sake wani gwajin. Sai dai karamin ministan tsaron Koriya ta Kudu Jang Kyoung-Soo ya yi wani taron manaima labarai a birnin Seoul inda ya ce ya na da kwararun shaidu da ke nuna cewar Koriya ta Arewa za ta yi sabon gwaji nan bada jimawa ba.

Tuni dai Rasha ta yi kira da a tattauna da Koriya ta Arewa idan ana son samun mafita ga rikicin nukuliya da ake fuskanta da ita sannan ta caccaki Amirka dangane da barazanar amfani da karfin kan shugaba Kim Jong-Un. Sai dai shugabannin kasashen BRICS da ke samun habakan tattalin arziki cikin hanzari ciki har da Afirka da Kudu da China da Brazil sun nuna rashin jin dadinsu kan gwajin makamin kare dangi da Koriya ta Arewa ta yi. hasali ma shugabannin kasashen sun yi kira da a zauna kan teburi guda don samun mafita ga rikicin nukiliyar maimakon kakaba takunkumai ko amfani da karfi kamar yadda aka saba.