Jam'iyyar da ke mulki a Koriya ta sha kaye a zaben majalisa
April 11, 2024Talla
Kafofin yada labaran kasar sun ce shugaba Yoon, na jam'iyyar PPP da ke yin mulki, wanda aka zaba a shekara ta 2022,ya zama shugaban kasar Koriya ta Kudu na farko da jam'iyyarsa ta rasa rinjaye a majalisar dokokin. Masu aiko da rahotannin sun ce shugaban jami'yyar ta masu ra'ayin rikau,zai gamu da babban cikas wajen aiwatar da manufofinsa a tsawon wa'adin mulkinsa,wajen aiwatar da dokoki da kasafin kudi saboda rashin rinjayen.