1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaKoriya ta Kudu

Koriya ta Kudu ta kulla sabuwar alaka da kasashen Afirka

Fauziyya Dauda Abdoulaye Mamane(Sulaiman Babayo)
June 5, 2024

Kasar Koriya ta Kudu ta karbi karbar bakuncin gomman shugabannin Afirka da ke halartar taron koli na Koriya da Afirka wanda ke gudana a babban birnin kasar.

https://p.dw.com/p/4gfLO
Äthiopien I Unterzeichnung eines Finanzierungsabkommen über 1 Milliarde Dollar
Hoto: Office of the Prime Minister-Ethiopia

A yayin taron koli a kan kasuwanci, wanda shi ne irinsa na farko a tsakanin  Koriya ta Kudu da kuma kasashen Afirka 48, kusan yarjejeniyoyi 50 ne bangarorin biyu suka cimma a tsakaninsu domin karfafa hadin gwiwar cinikayya a fanonnin makamashi da hako mai da ma sarrafa kayayyaki.

A yanzu haka, kamfanin Hyosung Corp na Koriya ta Kudu, ya sanya hannu kan yarjejeniyar tura na'urorin transformer wanda darajarsu ta kai dala miliyan 30 zuwa kasar Mozambique, kana ma'aikatar kula da harkokin masana'antu ta kasar ta sanar da cewa ta sanya hannu kan yarjejeniyoyin hadin gwiwar samar da ma'adanai da kasashen Madagascar da kuma Tanzaniya, domin samar da wasu ababen kamar batira.

Karin bayani : Koriya ta Kudu da Kasashen Afirka za su karfafa dangantaka

Shugaban Koriya ta Kudu Yoon Suk Yeol
Shugaban Koriya ta Kudu Yoon Suk YeolHoto: JEON HEON-KYUN/Pool/REUTERS

Shugaban Koriya ta Kudu, Yoon Suk Yeol ya ce zai fadada taimakon kasar na raya kasashen Afirka zuwa dala biliyan 10 cikin shekaru shida masu zuwa yana mai cewa "Rawar da Afrika ke takawa na samun karbuwa duk da rashin tabbas da ake da shi a bangaren samar da kayayyaki sakamakon tashe-tashen hankula da ake fama da su a wasu sassan. Ina fatan za mu kara fadada cin moriyar juna ta hanyar karfafa dangantaka da manyan kasashen Afirka kan ma'adanai da kuma kawancen ma'adanai na tsaron wanda shi ne hadaka a tsakanin kasashen da ke cinikayya."

Gwamnatin Seoul da ta dogara a yanzu da China, tana son inganta dangantaka da Afirka a fannonin albarkatun kasa da kuma ma'adanai da nufin fadada jajjircewarta a manyan masana'antun fasaha.

Su ma kasashen Afirka da suka halarci taron da ke zama na hudu mafi girma a nahiyar Asiya na maraba da wannan sabon hadin gwiwa.

Karin bayani : Koriya ta Arewa: Inganta noman shinkafa a kasashen Afirka

Shugaban Kungiyar Tarayyar Afirka Mohamed Ould Ghazouani
Shugaban Kungiyar Tarayyar Afirka Mohamed Ould GhazouaniHoto: GABRIEL BOUYS/AFP/Getty Images

A jawabin shugaban kungiyar Tarayyar Afirka AU kana shugaban kasar Mauritaniya Mohamed Ould Ghazouani, ya ce kasashen na son yin koyi da kwarewar Koriya ta Kudu wajen samar da ci gaba ga fannin masana'antu da ma ci gaban fasahar zamani yana mai cewa "Ina da kwarin gwiwar cewa, ya na da matukar mahimmanci a kara karfafa jarin da Koriya ta Kudu ke zuba wa a Afirka, tare da tabbatar da cewa kamfanonin kasar sun yi amfani da damarsu da suka bayar wa ga kasuwannin nahiyar, musamman ma a manyan fanonnin da suka hada da masana'antu da ayyukan gona da kuma fasahar tattalin arziki na zamani da ma cimma ci gaba mai dorewa."

Bangarorin biyu na fatan su gaggauta tattaunawar da suke yi kan hadin gwiwa na habaka tattalin arziki, ciki har da tallafin dala biliyan 14 da Koriyar za ta bayar domin fitar da kaya zuwa domin a inganta kasuwanci da kuma zuba jari a kamfanoninta da ke nahiyar Afirka.