1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Moritaniya: Sai an sake salon yaki da ta'addanci

February 26, 2020

Shugaban kasar Moritaniya Mohamed Ould Cheikh El Ghazouani, ya yi kiran kasashen yankin Sahel da su sake dabara a bangaren yaki da ayyukan 'yan bindiga da suke ciki.

https://p.dw.com/p/3YROC
Afrika | Burkina Faso | Soldaten im Einsatz in Bobo-Dioulasso
Hoto: Imago Images/ZUMA Press/D. White

Shugaban na Moritaniya ya yi kiran ne lokacin taron koli na yini guda da kasahen suka yi a kasar, ganin yadda ake ci gaba da asarar rayuka gami da tabarbarewar tattalin arziki.

Shi ma shugaban hukumar Tarayyar Afirka Moussa Faki Mahamat, ya jaddada bukatar ganin kasashen sun ci galaba a yaki da suke yi da 'yan bindiga ala-kulli halin.

Shekaru takwas ke nan kasashen na Sahel da suka hada da Burkina Faso da Chadi da Mali Moritaniya da Nijar ke fama da matsalolin na tsaro.

Kimanin mutum dubu hudu ne suka mutu a bara kadai a tsaknin kasashe uku na yankin, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.