Koriya ta Kudu za ta afka wa ta Arewa
August 10, 2017Talla
Kasar Koriya ta Kudu ta ce a shirye ta ke da ta afkawa makwabciyarta Koriya ta Arewa, bayan fitowar sanarwar Koriya ta Arewar kan shirinta na farwa tsibirin Amirka na Guam. Wani kakakin manyan hafsoshin Koriya ta Kudun, ya ce a duk lokacin da suka hango alamun hari daga Koriya ta Arewan, to la budda za su kai mata hari ba tare da wata-wata ba.
A baya dai Koriya ta Arewa ta yi barazana kan yankin na Guam, bayan kafa wani sansanin kare kai daga harin makami mai linzami da Amirka ta yi shekaru hudun da suka gabata.