1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu ta ci 'yan sanda tara kan kisan 'yan Shi'a

June 29, 2020

Kusan shekara guda da kisan wasu 'yan Shi'a da ke muzahara a Najeriya, kotu ta yanke hukuncin tilasta 'yan sanda biyan diyyar rayukan da suka kashe a Abuja.

https://p.dw.com/p/3eXR9
Nigeria Abuja Proteste von Schiiten des Islamic Movement
Hoto: picture-alliance/AA/A. A. Bashal

Babbar kotu da ke Abuja a Najeriya, ta ci rundunar ‘yan sandan Najeriyar tara ta Naira miliyan 15 bisa zargin kashe ‘ya'yan kungiyar ‘yan Shi’a ta IMN su uku, a wata zanga-zangar da suka yi a ranar 23 ga watan Yunin bara.

Mai Shari’a Taiwo Taiwo wanda ya yanke hukuncin a Abuja, ya bukaci rundunar ‘yan sandan da ta biya iyalan mutanen uku Naira milyan biyar kowanensu, ya kuma bukaci babban asibitin da ke Abuja da ya bai wa ‘yan uwansu gawarwakin mutane da ke ajiye a asibitin.

Sai dai alkalin ya ki amsa bukatar rundunar ‘yan sandan ta neman gafarar abin da ta aikata.

Muhammad Ibrahim Gamawa shi ne mai magana da yawun kungiyar ‘yan uwa Musulmi ta IMN, kuma ya shida wa wakilinmu da ke Abuja Uwaisu Abubakar Idris, cewar abin farin ciki shari'ar kuma tabbaci ne cewa ba su taka dokar ba.