1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Kotu za ta fara sauraron shari'ar Isra'ila a kan Falasdinu

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
February 19, 2024

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci kotun ta yi nazari game da zargin da ake yi wa Isra'ila na cin zarafin al'ummar Falasdinu, da kuma yadda ta mamaye wasu yankunan kasashen Larabawa a shekarar 1967

https://p.dw.com/p/4cYm2
Hoto: Piroschka van de Wouw/REUTERS

A Litinin din nan ce kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICJ za ta fara sauraron shari'ar halascin mamayar da Isra'ila ta yi wa yankunan Falasdinawa tun daga shekarar 1967, inda kasashe 52 za su ba da shaida, wadanda suka hada da Amurka da Rasha da Chaina.

Karin bayani:ICJ ta yi watsi da bukatar karin kariya ga Falasdinawa

Wannan na zuwa ne kwanaki uku bayan da kotun ta yi watsi da bukatar kasar Afirka ta Kudu da ke neman sanya wa Isra'ila karin ka'idoji kan mamayar da take ci gaba da yi wa Falasdinawa a Gaza.

Karin bayani:Isra'ila za ta bayyana a gaban kotun kasa da kasa

Babban zauren Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci kotun ta yi nazari game da zargin da ake yi wa Isra'ila na cin zarafin al'ummar Falasdinu, da kuma yadda ta mamaye wasu yankunan kasashen Larabawa a cikin shekarar 1967 ta mayar da su cikin ikon ta.