Kotun Pakistan ta daure tsohon firaminista Khan da matarsa
January 17, 2025Wata kotu a Pakistan ta yanke wa tsohon Firaminista Imran Khan hukuncin daurin shekaru 14 a gidan yari, bisa samunsa da laifin cin hanci da rashawa da ke da alaka da binciken badakalar kudi da aka gudanar. Alkali Nasir Javed Rana ne ya yanke hukuncin a wata kotun da aka kafa a cikin gidan yarin da Khan ke tsare, inda ya same shi da wani karin laifi na amfani da mukaminsa na firayiminista ba bisa ka'ida ba.
karin bayani: An haramta wa Imran Khan rike mukami a Pakistan
Sannan mai shigar da kara Muzaffar Abbasi ya shaida wa manema labarai cewar an yanke wa mai dakin Khan, wacce ita ma ake tuhuma a shari'ar, hukuncin daurin shekaru bakwai a gidan yari saboda ta taimaka wajen aikata laifi. Sai dai lauyansa Faisal Chaudhry ya ce jam'iyyar Imran Khan na da niyyar kalubalantar hukuncin a kotu na gaba, saboda taba alakanta hukunci da bita da kullin siyasa.