1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwankwaso ya magantu kan kawancen neman mulki a 2027

Uwais Abubakar Idris MAB
December 30, 2024

Jigon jam'iyyar NNPP mai adawa a Najeriya Rabiu Musa Kwankwaso ya yi bayani kan hada kai da Atikiu Abubakar na PDP da Peter Obi na Labour domin tinkarar APC a zaben 2027, musamman batun fitar da dan takara daya tilo.

https://p.dw.com/p/4ognL
Rabiu Musa Kwankwaso, jigo na jam'iyyar adawa ta NNPP a Najeriya
Rabiu Musa Kwankwaso, jigo na jam'iyyar adawa ta NNPP a NajeriyaHoto: Uwais Abubakar Idris/DW

Tun bayan kammala shari'un da suka tafka da jam'iyyar APC da ke mullki a Najeriya, jam'iyyun adawa na kasar ke ta zawarcin juna musamman manya na jam'iyyar PDP da Labour da NNPP, a kokarin fara shiri tun da wuri don ka da dare ya yi masu a kan yadda za su tinkari babban zaben 2027. Wannan ya sanya ganawa tsakanin wasu daga cikin shugabannin jam'iyyun adawa da suka hada da Peter Obi na jam'iyyar Labour da Atiku Abubakar da ke zama tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriyar na jam'iyyar PDP.

Karba-karba tsakanin PDP da NNP da Labour?

Peter obi ne ya yi takarar shugabancin Najeriya a jam'iyyar Labour a zaben 2023
Peter obi ne ya yi takarar shugabancin Najeriya a jam'iyyar Labour a zaben 2023Hoto: Katrin Gänsler/DW

Bayanai sun ambato cewa an kai ga cimma wata yarjejeniya ta tsarin karba-karba a tsakaninsu, inda Atiku zai yi shekaru hudu, sannan Kwnakwaso ya yi mulki na shekaru hudu daga baya kuma ya bai wa Peter Obi dama ya yi shekaru takwas. Dr Rabiu Musa Kwankwaso  da ke zama jigo a jam'iyyar NNPP wanda aka ambato an cimma wannan yarjejeniya, ya bayyana gaskiyar wannan tsari, inda ya ce: " Ni ban zauna da ko su Peter Obi ko su Atiku a kan a zauna a yi wata yarjejeniya ko wata ka'ida ba,.. Na yi mamakin yadda mutane a irin wannan matsayi za su rinka fadan abin da ba'a yi ba."

Karin bayani: Zargin Kwankwaso da neman yin katsalandan a shugabancin Kano

Jam'iyyun adawa na Najeriya sun dade suna kokarin hada kai a tsakaninsu tun a zabubbukan 2019 da 2023, amma duk kokarin da suka yi ya ci tura. A kan samu rarrabuwar kawuna a tsakaninsu tare da zargin jam'iyya da ke mulki da lalata musu tsari, kamar yadda Hassan Sardauna mai sharhi a kan al'amurran yau da kullum a Najeriya ya yi tsakaci a kai, inda ya ce: "Manyan Najeriya na jam'iyyun adawa, abin da suka sa a gaba shi ne son kai da bukatar son kai."

Kwankwaso na da niyyar nada gwiwa da Sauran a 2027?

Wa zai zama gwani a 2027 tsakanin Bola Tinubu da Rabiu Kwankwaso da Atiku Abubakar?
Wa zai zama gwani a 2027 tsakanin Bola Tinubu da Rabiu Kwankwaso da Atiku Abubakar?

Sunan Dr Rabiu Musa Kwankwaso ya dade yana amo a kokarin ganin sun yi tafiya tare da Atiku Abubakar, amma hakan ba ta samu ba, shin a yanzu idan aka yi ma sa tayi su tafi tare zai amince duk da cewa yana koke ba'a yi wancan zama da shi ba? Dr Rabiu Musa Kwankwaso da ya yi mata takarar neman shugaban kasa a zaben 2023 ya ce: "Shi wannan maganar haduwa, mun ce hannunmu a bude yake, amma wannan abin da suke yi da ya shafi karya ko zalunci, wannan ya dada raba mu da tsarin da suke yi."

Karin bayani: Kwankwaso ya sanar da ficewa daga PDP

Akwai sauran kusan shekaru uku kafin gudanar da zaben shugaban kasa a Najeriya a 2027, amma tuni hankula suka karkata a kansa kama daga bangaren jam'iyya mai mulki da ke ambata babu wuri da wani zai shiga ,da ‘yan adawa da ke bayyana cewa kan ‘yan Najeriya ya waye, saboda sun san inda za su dosa da kuri'unsu saboda halin da kasar ke ciki.