Macron: Faransa za ta yanke shawara kan Nijar
September 1, 2023Yayin da dangantakar Nijar da Faransa ke kara tsami, Shugaba Emanuel Macron ya ce Faransa za ta yanke shawara kan makomar huldarta kasashen biyu ne kawai bayan ya tattauna da hambararren shugaba Mohamed Bazoum, wanda sojoji ke ci gaba da tsarewa tun bayan kifar da gwamnatinsa a ranar 26 ga watan Juli da ya gabata.
Karin bayani: Takun saka tsakanin Nijar da Faransa
Furucin na shugaba Macron na zuwa ne a daidai lokacin da takun saka ke kara kamari tsakanin sabbin jagororin sojan Nijar da fadar Elysée a ta fuskar diflomasiyya ciki har da batun korar jakadan Faransa da kuma soke wasu yarjejeniyoyi da kasashen biyu suka rattaba a baya.
Karin bayani: Nijar ta umarci yan sanda su fitar da Jakadan Faransa
Macron ya kuma jaddada goyoyn baya ga dukannin matakan da ECOWAS ta dauka a kan Nijar ciki har da takunkuman masu tsanani don yin matsin lamba ga sojoji na su dawo da hambararren shugaba kan kujerarsa.
Karin bayani: Matsin lamba kan sojojin da suka yi juyin mulki
To sai dai yayin da yake tsokaci kan sabuwar matsayar da shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya sanar a jiya kan cewa sojoji Nijar su mika mulki ga farar hula bayan rikon kwarya na watanni tara, Marcon ya ce ba abu bane da ya dame shi idan har bai saba wa dokoki da kuma hakkin al'umma ba.