1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Yanayin tsaro na ci gaba da haddasa mahawara

February 11, 2020

Al’ummar Arewa maso gabashin Najeriya da ma na sauran sassan arewacin kasar sun bayyana kasawar gwamnatin Najeriya wajen samar musu da tsaro daya daga cikin manyan alkawuran da ta yi yayin yakin neman zabe.

https://p.dw.com/p/3Xd1D
Nigeria | Niedergebrannte Fahrzeuge in Auno
Hoto: Getty Images/AFP/A. Marte

Wannan dai ya biyo bayan karuwar hare-haren da mayakan Boko Haram ke kaiwa ne a sassan Arewa maso Gabas da kuma kuma yadda masu kame mutane suna garkuwa da su ke kara samun gindin zama a wasu jihohin Arewa maso yammacin Najeriyar. Daga cikin abubuwan da Shugaban Muhammadu Buhari ya alkwari yayin da yake son al’ummar Najeriya ta ba shi damar karbar jagorancin kasar shi ne tabbatar da tsaro musamman a shiyyar Arewa maso gabashin Najeriyar inda rikicin Boko Haram ya gurgunta harkokin rayuwa da na ttalin arzikin kasa. An samu saukin matsalolin a shekarun farkon wa’adinsa inda hare-haren Boko Haram suka takaita a Jihohin Borno da Yobe sai kuwa wani bangare na Jihar Adamawa.

Nigeria Baga | Truck des IS Gruppe (ISWAP)
Hoto: Getty Images/AFP/A. Marte

To sai dai ana kokarin magance matsalar Boko Haram a shiyyar Arewa maso Gabas sai kuma matsalar sace mutane a yi garkuwa da su domin kudi ta bullo a yakunan Arewa maso Yamma da kuma rikicin makiyaya da manoma da rikicin kabilanci a jihohin Arewa ta Tsakiya. Yanzu haka kuma hare-haren Boko Haram sun tsananta a sassan jihar Borno inda ko a farkon makon nan mayakan sun hallaka mutane sama da 30 tare yin awon gaba da mata da yara da kona motoci da gidaje dama a garin Auno da ke kusa da Maiduguri kan hanyar zuwa Damaturu. Wannan na wakana ne a daidai lokacin da gwamnatin Najeriyar ta dauki matakin bude hanyoyin Damboa da Gamboru da sunan cewa an samun ingantuwar harakokin tsaro a yankin.

A ‘yan kwanakin nan dai an shaida gwanin gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum yana ta da jijiyoyin wuya kan yadda ake harkokin tsaro ke tafiya inda ya koka kan yadda sojoji ke karbar kudade a hannun matafiya da ma yadda ake samun karancin sojojin a wasu sassan jihar.Sai dai a nasu bangaren jami’an tsaro Najeriya na ganin sun tabuka abin kirki wajen yaki da Boko Haram ta yadda ba su da karfin kai hare-hare ko kuma kame wurare kamar yadda suke yi a baya.
  
Duk da wanann tabbaci mazauna wannan hanya musamman mutanen garin Auno da wasu kauyuka da ke kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu sai da suka yi wata zanga-zanagr nuna damuwa kan kashe-kashen da ake yawan samu sanadiyyar hare-haren mayakan Boko Haram, da kuma rufe hanya da sojoji ke yi daga karfe biyar na yamma.

Nigeria Präsident Buhari
Hoto: Reuters/L. Gnago