1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAmurka

Mai yunkurin halaka Donald Trump ya gurfana a kotu

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
September 16, 2024

Routh ya yi kokarin harbe Donald Trump ne bayan da ya lababa da bindiga cikin dajin da Trump din ke wasan kwallon Golf

https://p.dw.com/p/4kgy4
Hoto: Kamil Krzaczynski/AFP/Getty Images

Mutumin nan da ake zargi da yunkurin halaka tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya gurfana a gaban kotu yau Litinin, inda aka tuhume shi da laifin mallakar makamai marasa sahihiyar lamba, sai kuma wasu tuhume-tuhume da za su biyo baya nan gaba idan binciken ya yi nisa.

Karin bayani:Trump ya sake tsallake rijiya da baya a yunkurin halaka shi

Ryan Routh mai shekaru 58 a duniya, ya bayyana ne gaban kotun sanye da bakaken kaya na 'yan kurkuku, hannayensa da kafafuwansa daure da sasari.

Routh ya yi kokarin harbe Donald Trump ne a ranar Lahadi, bayan da ya lababa da bindiga cikin dajin da Trump din ke wasan kwallon Golf a Florida, kuma kan ka ce kwabo jami'an tsaro suka hango shi kuma sun harba bindiga, daga nan ne ya arce a mota ya bar kayansa da kuma bindiga, kafin daga bisani su kamo shi.

Karin bayani:Shugabannin duniya sun yi tir da harin da aka kai wa Trump

Wannan dai shi ne karo na biyu cikin watanni biyu da aka yi yunkurin halaka Donald Trump, bayan na ranar 13 ga watan Yulin da ya gabata, wanda aka harbe shi a kunne, lokacin da ya ke tsaka da jawabin yakin neman zaben shugaban kasa a Pennsylvania.

Ranar 5 ga watan Nuwamba mai zuwa ne za a gudanar da zaben shugaban kasa a Amurka, wanda Mr Trump yake yi wa Republican takara, yayin da mataimakiyar shugaban kasa Kamala Harris ke takara karkashin jam'iyyar Democrats mai mulkin kasar.