1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar Dinkin Duniya ta ce tsagaita wuta a Zirin Gaza

December 12, 2024

Majalisar Dinkin Duniya ta sake amincewa da bukatar tsagaita wuta nan take ba kuma tare da wani sharadin ba a Zirin Gaza. Wani zama da kasashe mambobi suka yi ne ya amince da ahakan a ranar Laraba.

https://p.dw.com/p/4o2Iz
Hoto: Bianca Otero/ZUMA Press Wire/picture alliance

Tsagaita wutar wadda Majalisar Dinkin Duniyar ke cewa ta dindindin ce, ta kuma kunshi batun sakin wadanda ake garkuwa da su a yakin Isra'ila da kungiyar Hamas a Gazar.

Kasashe mabobi 158 ne dai jami'an, suka amince da daftarin dokar, yayin kuma da kasashe tara da suka hada da Amurka da Isra'ila su ne suka bijire, sannan 13 suka kaurace wa kuri'ar da aka kada a jiya Laraba.

Sai dai a bara ma dai taron Majalisar Dinkin Duniyar ya amince da batun tsagaita wutar har sau biyu, ba kuma tare da an martaba shi ba.

Amma ana kallon a wannan karon, an yi amfani da lafuza masu karfi da ke iya tilasta tabbatuwar bukatun da aka yi nazari kansu da suka hada har da goyon baya ga hukumar agaji ta yankin Falasdinu UNRWA.