1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin shawo kan rikicin Sudan

May 11, 2023

Hukumar kare hakkin bil Adama ta Majalisar Dinkin Duniya, za ta yi zama domin duba halin da aka shiga a kasar Sudan, kamar yadda wasu majiyoyin diflomasiyya suka sanar.

https://p.dw.com/p/4RBcd
Hoto: AFP/Getty Images

Zaman wanda Jamus da sauran wasu manyan kasashe suka nuna bukatar da a yi, zai maida hankali ne a kan yakin tare da jaddada bukatar kiyaye hakkokin fararen hula kamar yadda yake cikin dokokin kasashen duniya.

Sai kuma a share guda, akwai wasu kasashen da ba su amince da wannan bukata ba, suna mai ganin hakan tamkar shiga harkokin cikin gida ne na wasu kasashe.

Daruruwan mutane ne dai suka mutu a yakin Sudan da ya faro ranar 15 ga watan jiya, wasu sama da dubu 700 kuma suka tsere.

Majalisar Dinkin Duniya dai ta ce Sudan mai mutum miliyan 19 da kuma ke cikin jerin kasashe matalauta a duniyar, tana kan hadarin fuskantar yunwa sakamakon wannan yaki.