Martani game da karar Afirka ta Kudu kan Isra'ila
May 17, 2024Bayan da Babbar Kotun Majalisar Dinkin Duniya ta kwashe kwanaki biyu ta na sauraran karar da Afirka Ta Kudu ta shigar gabanta kan zargin Isra'aila da kisan kare dangi a yankin Gaza da kuma bukatar tilasta wa Israila dakatar da farmaki kan yankin Rafah. Isra'ilar dai ta musanta wannan zargi duk da ta tabbatar da cewa Falasdinawa na zaune cikin halin ni yasu a yankunan da ta ke mamaye da su.
Karin Bayani: Isra'ila za ta kare matsayarta a kotun duniya
Watanni biyar bayan da kotun duniya ta nemi Isra'ila ta guji aikata duk wasu ayyukan da za,a siffanta su da kisan kare dangi kan al'ummar Falalsdinawan Gaza, kasar Afirka ta Kudu,wacce a baya ta shigar da kara don taka wa Isra'ila birki kan abun da ta kira kisan kiyashin da take yi wa Falalsdinawa, ta sake maka kasar ta Isra'ila gaban kotun ta duniya a karo na hudu bayan wannan kiran da kotun ta yi wa Isra'ila, kuma kamar yadda mai gabatar da kara na Afirka Ta Kudu, Visu Madonsela ke cewa, bai san abin da za a kira kisan kiyashi ba, muddin ba,a siffanta abin da Isra'ila ke yi wa Falalsdinawan Gaza da Rafah kisan kare dangi ba:
Karin Bayani: ICJ ta umurci Isra'ila ta bude karin hanyoyin shiga Gaza
"Abin takaici, an sake tilasta wa kasarmu Afirka ta Kudu sake bayyana gaban wannan kotu don rokonta da ta tilasta wa Isra'ila dakatar da yakin da ta kaddamar kan yankin Rafah, don aiwatar da yarjejeniyar kasa da kasar da ke hana kisan kare dangi. Domin a yanzu haka, bayan kashe fiye da mutane 35,000 da Isra'ila ta yi a Gaza, na galibin yara kanana da mata da tsofaffi, galibin kasashen duniya da ma kungiyoyin kasa da kasa masu zaman kansu, sun tabbatar da cewa, abin da Isra'ila ke yi a yankin Gaza, ba kare kai ba ne, kisan kiyashi ne da ya kai da a siffanta shi da kisan kare dangi. Don haka muka sake yunkurowa don sauke wannan nauyi da ya rataya a wuyanmu, na ganin kotun duniya ta ba da umarnin dakatar da wannan kisan kare dangin da ake ci gaba da yi."
Karin Bayani: Martani kan kiran da Kotun duniya ta yi wa Isra'ila
Bugu da kari, Afirka ta Kudu ta bukaci kotun da ta umarci Isra'ila bayan janyewa daga Rafah ta dauki matakan tabbatar da jami'an Majalisar Dinkin Duniya da ma'aikatan jinya da 'ya jaridu su shiga yankin Gaza, sannan ta ba su rahoto cikin mako guda kan yadda ta ke aiki da wannan bukata. To sai dai kamar yadda Lauyan Isra'ila,Tamar Kaplan-Tourgeman, ya siffanta zarge zargen na Afirka ta kudu da shakulatun bangaro:
"Wannan tuhumar da ake mana, tun ma daga jin sunanta, ka san tsagwaron sharri ne da gina maganganu bisa son rai gami da kin yin la'akari da abin da ke gudana a kasa. Sojojinmu na kaddamar da farmakin murkushe yan ta'addan da suka kai wa al'ummarmu hari suka kashe fiye da mutane dubu daya, kana suka yi garkuwa da wasu daruruwan. Muna kuma fatattkar wadannan yan ta'adda ne a cikin biranen da ke cike da fararen hula, wadanda su ma yan ta'addan ke garkuwa da su. Mu kan yi gargadi kafin kaddamar da hare harenmu kamar yadda muke amfani da makaman da barnarsu ke takaita ga inda muka nufa. Amma hakan baya nufin ritsa wa da fararen hula bisa kuskure, wanda hakan tabbas abin takaici ne. Saboda haka, siffanta kokarin kare kanmu daga yan ta'adda da cewa hakan kisan kiyashi ne tsagwaron karya ce. Maimata karya akai akai ba zai taba mayar da ita ta zama gaskiya ba."
Wasu kasashen dai irin su Cuba da Venanzuala da Masar da Libiya sun bi sawun Afirka ta kudu wajen hada karfi da karfe don maka Isra'ila gaban kotu don ta dakatar da yaki kan Gaza, bayan da kwamatin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya gaza har sau hudu wajen tilasta wa Isra'ila dakatar da yakin.
Masana shari'a dai na nuna shakkunsu wajen iya gamsar da kotun da kwarararan hujjojin da za su sanya kotu tursasa wa Isra'ila dakatar da yakin nata kan Gaza, kuma ko da kotun ta yanke hukuncin hakan, kotun bata da hurumin zartar da dokar da ta yanke hukunci kanta, kamar yadda ya faru ga Rasha, wacce duk da kotun ta bata umarnin dakatar da yaki kan Ukrain, Rashan ta yi fatali da umarnin ba tare da an dauki wani mataki kanta ba.
Masharhanta dai irinsu Rosie Brichard ta tashar DW na daukar yunkurin na Afirka Ta Kudu da wani motsin da ya fi labewa:
"Duk da cewa kotun ta duniya bata da karfin tursasa aiwatar da umarninta kan kasashe, sai dai karar ta Afirka Ta Kudu kan iya zama wani karin matsin lamba kan Isra'ila da sake mayar da ita saniyar ware a daidai lokacin da ake samun takun saka kan ci gaba da wannan yakin tsakaninta da kawayenta, wadanda ke ta yi mata kira ta dakatar da shi."