1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matashi ya kaddamar da wasannin bidiyo na Afirka

August 2, 2022

A wannan Litinin ne aka kaddamar da dandalin samun wasannin kwamfuta da matashi Teddy Kossoko ya samar. Matashin dai na da niyyar tallata Afirka ne da kuma samun kudade.

https://p.dw.com/p/4Ez0p
Gara-Shops auf Tablet und Mobiltelefon
Hoto: Maseeka Game Studio

Bayan fahimtar cewa manya-manyan shagunan manhajojin sadarwar zamani ba su damuwa da wasu fasahohi daga nahiyar Afirka ne, ya sanya Teddy Kossoko dan asalin kasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya yunkurawa domin samar da manhajar Android musamman saboda fasihai daga nahiyar su fara samun miliyoyin kudaden da ake samu a bangaren yanzu a duniya.

Shagon ko dandanlin da ya samar da aka kaddamar a yau Litinin mai suna Gara Store, za ta shiga sahun shagunan manhajoji a wayoyin hannu da kuma kwamfuta, da nufin samun kudade a duk lokacin da wani ya kalli bidiyo ko ta’ammali da dandalin.

A shekarun baya Kossoko ya samar wani da manhajar wasannin bidiyo na  Masseka Game Studio, ya fara ne da dora ta a dandalin Google Play Store domin tallata wasannin da suka shafi Afirka da za su daga darajar nahiyar. Amma a cewar Teddy Kossoko abin bai yi tasirin da yake tunani ba saboda rashin biyan kudade ta hanyar amfani da katunan banki a Afirka.

Gara Store-Schnittstelle auf dem Mobiltelefon
Hoto: Maseeka Game Studio

Shekaru hudu ne dai Teddy Kossoko ya kwashe kafin ya iya hada dandalin Gara Store, kuma aiki ne da ya lakume euro miliyan guda kafin a kai ga hada shi.

Kiyasi kuma ya nuna 3% ne kacal na mutanen Afirka kudu da hamadar Sahara da ke amfani da katunansu na banki wajen sayen kayayyaki ta intanet musamman katin karbar rance na Credit Card.

Matashi Teddy, Kossoko, na mai ra’ayin cewa tsarin tafiyar zamanin yau da ake da sabbin abubuwa da ke fitowa kusan kullum, ba za cire tsammanin gamuwa da cikas ba. Sai dai duk da hakan giwowinsa ba za su yi sanyi ba.

Duk dai da tarin matsalolin da matashin ke cin karo da su a wannan harka, Teddy Kossoko na da kwarin gwiwar ce a karshe wannan dandali na wasanni Game da ya shafi al'amura daga Afirka a dandalinsa na Gara Store zai yi nasarar da za ta kai mataki na duniya.