1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamhuriyar Afirka ta Tsakiya

Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya: Fashewar nakiya

February 15, 2024

Nakiyoyi na ci gaba da kashe mutane a garin Paoua da ke Arewa maso Yammacin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, abin da ke shafar tattalin arzikin yankin musamman fannin noma.

https://p.dw.com/p/4cRkd
Afirka ta Tsakiya | Shugaban Kasa | Faustin-Archange Touadéra
Shugaban Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Faustin-Archange TouadéraHoto: Präsidentschaft der Republik Ruanda

Matsalar fashewar nakiyoyin dai ta sanya Hukumar Majalisar Dinkin Duniya da ke Kula da Ma'adanai UNMAS, kokarin kare al'umma. Garin na Pougol na da nisan kilomita 41 da birnin Paoua, inda a ranar 15 ga watan Janairun da ya gabata wata nakiya ta tashi da wasu sojojin Majalisar Dinkin Duniya 'yan kasar Kamaru lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa garin Mbindale tare da halaka soja guda da kuma jikkata wasu biyar. Irin wannan al'amarin na kawo cikas kan harakokin kai kawo, inda masu sana'ar abubuwan cimaka ke fuskantar matsala a cikin jihar sakamakon fargabar fadawa cikin hadari a kan hanya da ma su saye kan yi. Wata 'yar kasuwa Salva Kpa ta ce, wannan al'amarin ya sa ta canza hanyar samar da kayayyaki.

Jahuriyar Afirka ta Tsakiya | Paoua | Noma
Garin Paoua na da manoma da damaHoto: Barbara Debout/AFP/Getty Images

#b#Daya daga cikin ma su motocin zirga-zirga Lucien Mbaïgoto ya nunar da cewa, ma su sayen kaya da dama ba sa son yin kasadar zuwa jihar ta Paoua. Tun bayan taron kasa da kasa na shekarar 1997, aka haramta amfani da wa'dannan nakiyoyin. A cewar Hukumar Majalisar Dinkin Duniya UNMAS da ke da nauyin fidda nakiyoyi a yankin amfani da nakiyoyin na kara kamari, abin da ya sa ma'aikatansu da ke wurin ke wayar da kan jama'a kan hadarin da ke tattare da hakan. Al'amarin garin Paoua, misali ne guda daga manyan matsalolin da ke da alaka da nakiyoyi. A garin Boali da ke arewacin birnin Bangui fadar gwamnatin kasar, sojojin hayar Wagner na Rasha sun dauki matakai domin kare babban birnin na Afirka ta Tsakiya.