Yan gudun hijirar Chadi na son fara noma a Afirka ta Tsakiya
February 9, 2024A yankunan Bétoko da Bédaka da ke cikin jihar Paoua a arewacin Jamhriyar Afirka ta Tsakiyya, 'yan gudun hijira da suka fito daga kasar Chadi na neman izinin yin amfani da fillayen noma. Marina da ke zaman daya daga cikin 'yan gudun hijira ta ce: " Babban burinmu shi ne, mu tsara kanmu gungun-gungu na noma idan aka samar mana da filayen noma da kayan aiki : Hakan zai ba mu damar cin gashin kanmu tare da kare mutuncinmu da kuma daidaito a wannan duniya da rashin gaskiyya ya yi yawa''
Karin bayani: Sauyin yanayi ya shafi 'yan gudun hijira
Kusan 'yan gudun hijira 31,000 da suka fito daga kudancin Chadi ne ke zaune a jihar ta Paoua bayan da suka guje wa rikicin makiyaya da manoma . Jacqueline Kornandji da ta samu mafaka a jihar bayan da ta a rasa mijinta a tashin hankali ta ce: "Kannen mijina na gona domin kula da ita. Amma a ranar da misalin karfe biyu na rana, wasu Larabawa suka kewaye su, kafin su kashe daya daga cikinsu da adduna. Da mijina ya samu labari, sai ya je wurin da abin ya faru. shi ma aka yi masa kwanton bauna aka kashe shi. Gwamnatin Chadi na da hannu a kan a abin da ya faru "
Karin bayani: Rayuwar 'yan gudun hijira a Zambiya
Jacqueline na son ci gaba da ayyukan noma a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. Amma kafin ta samu izini daga hukumomi, a yanzu ta bude wani dan karamin wurin sayar da abinci. Saboda haka ne Olivier Fafa Attidza, wakilin hukumar kula da 'yan gudun hijira yake kokarin kwantar musu da hankula. Ya ce: " Muna goyon bayanku. Za mu yi duk kokarinmu domin kai namu goyon baya ga hukumomi da al'ummar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya domin taimaka muku duk tsawon kasancewarku nan."
Karin bayani: 'Yan gudun hijira na Sudan a Chadi
A garuruwan Bétoko da Bédaka, yawancin jama'a na daogara ne galibi da aikin gona. A yanzu kokarin da ake yi shi ne, na yin rigakafi ga afkuwar rigingimu tsakanin manoma da makiya: Shi ya sa hukumar 'yan gudun hijira ta MDD ke ci gaba da tattaunawa da al'umma domin samun fahimtar juna a kan batun rabon filayen noma ta yadda ko mai zai tafi lafiya ba tare da an samu tashin hankali ba.
Karin bayaniMatsalolin 'yan gudun hijira a Sakkwato:
Justin Malekian da ke da zama garin Paoua ya ce: " Hukumar da ke kula 'yan gudun hijirar da gwamnati za su iya shiga tsakani don nemo filiye, saboda matsalar fili ce ke haifar da rikici tsakanin 'yan gudun hijira da jama'a a gari. A wannan matakin ne ya kamata hukumomi su mayar da hankali sosai domin a samu isasshiyar mafita mai dorewa."
'Yan gudun hijirar sun gamsu da irin karbar da al'ummar yanki Paoua suka yi musu, inda suka tabbata cewar rayuwarsu za ta samu sauyi kuma za su samu biyan bukata cikin girma da mutunci.