1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mayakan Hezbollah sun harba rokoki zuwa arewacin Isra'ila

September 22, 2024

Kungiyar Hezbollah ta tsananta hare-hare zuwa Isra'ila da safiyar Lahadi, abin da ya sanya Isra'ila daukar matakan kare fararen hula da ke yankin cikin gaggawa.

https://p.dw.com/p/4kwSS
Wasu wuraren da Hezbollah ta ɓata a arewacin Isra'ila
Wasu wuraren da Hezbollah ta ɓata a arewacin Isra'ilaHoto: Shir Torem/REUTERS

Hukumar da ke kare fararen hula a Isra'ila ta bayar da umurnin rufe dukkanin makarantun da ke arewacin kasar, bayan wasu hare-haren rokoki da kungiyar Hezbollah ke harbawa zuwa cikin kasar.

Mayakan Hezbollah dai sun harba rokoki sama da 100 a wannan safiya inda wasu daga ciki suka fada birnin Haifa na arewcin Isra'ilar.

Wannan dai na nuna cikakkun alamu ne na kungiyar Hezbollah din ta fito yaki ne gadan-gadan, bayan kwashe watanni na alamun shika-shikan rincabewar rikici a tsakanin banagrorin biyu.

Rundunar sojin Isra'ila ta ce rokokin sun auni yankuna ne da galibnin gidajen fararen hula ke a cikin su.