MDD ta bukaci a tsayar da Isra'ila daga kai hari a Rafah
February 12, 2024Babban jami'in kare hakkin bil'adama na MDD Volker Turk ya bukaci manyan kasashen duniya da su dakatar maimakon ba da dama, yayin da firgicin kutsawa cikin yankin ke karuwa a tsakanin Falasdinawa sama da miliyan daya da suka makale a wannan yanki na kudu mai nisa.
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya sha alwashin tura sojojin kasa, zuwa yankin Rafah mai cunkoson jama'a a wani bangare na burinsa na kawar da kungiyar Hamas, abun da ya haifar da tsoro a duniya.
Yakin Gaza ya barke ne bayan da kungiyar Hamas ta kaddamar da wani hari da ba a taba ganin irinsa ba a Isra'ila a watan Oktoba wanda ya yi sanadin mutuwar mutane sama da dubu daya.
Yayin da kawo yanzu Isra'ila ke kan mayar da martani da hare hare ba kakkautawa a Gaza, wanda ya acewar ma'aikatar lafiyar yankin ya kashe sama da mutum du 28 galibi mata da kananan yara.