1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nadin sabon alkalin-alkalan Amirka

Usman Shehu Usman
February 1, 2017

Shugaban Donald Trump ya nada wani alkali mai ra'ayin rikau Neil Gorsuch a kotun kolin Amirka domin cike gurbin daya daga cikin alkalan kotun mai shari'a  Antonin Scalia wanda ya rasu a watan fabrairun bara.

https://p.dw.com/p/2WoD6
USA Trump Ernennung Neil Gorsuch
Hoto: Reuters/K. Lamarque

Tuni dai zaben sabon alkalin wanda ake yi wa kallon zai iya sauya fasalin bangaren shari'ar ya fara haifar da takaddamar a tsakanin 'yan jam'iyyar Demokrats. Mai shekara 49 da haihuwa Neil Gorsuch shi ne alkalin kotun koli mafi karancin shekaru da aka nada a Amirka cikin shekaru 20 da biyar da suka wuce.

Da yake jawabi a lokacin da ya bayyana nadinsa a kotun kolin Amirka, Gorsuch yace Trump da ma'aikatansa sun yi masa babban karamci, yana mai cewa yana sane da cewa tara yake bai cika goma ba, amma yana mai alkawarin yin aiki tukuru bisa tafarkin kundin tsarin mulkin Amirka. 

" Ya ce na yi alkawari idan aka tabbatar da ni zan yi dukkan abin da doka ta bani karfin iko na kasance mai biyayya ga kundin tsarin mulki da kuma dokokin wannan babbar kasa ta mu."

Sai dai tuni nadin wanda ya zo da ba za ta ya fara da fuskantar turjiya daga masu adawa, wadanda suka ci alwashin kalubalantar kusan dukkan wani nadi na alkalin kotun kolin da gani tamkar an yi musu fashinsa ne, kasancewar a baya tsohon shugaban kasar Barack Obama ya nada alkali Merrick Garland domin cike gurbin.