1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amincewa da dokar zabe a Najeriya

February 25, 2022

Bayan share tsawon lokaci cikin rudani, shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya rattaba hannu a kan dokar zaben kasar ta shekarar bana da Abujar ke fatan gina tsarin zaben shekarar badi da ita.

https://p.dw.com/p/47csv
Najeriya I Dokar Zabe
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince, tare da rattaba hannu a dokar zabeHoto: Nigeria Prasidential Villa

An dai kai har ga yin jerin zanga-zanga ta kungiyoyin fararen hula, domin tilastawa shugaban rattaba hannu a kan dokar mai tasiri. A baya dai Shugaba Muhammadu Buhari ya sa kafa ya take dokar da ta share tsawon lokaci a kuryar daki, kafin ya sanya hannun da ake ganin hakan na shirin bude sabon babi a cikin harkar zaben da ta dauki lokaci cikin rudani. Wani rikici a tsakanin gwamnoni da masu dokar tarayyar ne dai, ya kai ga sakaya wani sashe da ya haramtawa nadaddu na siyasar a matakin tarayya da jihohi da ke da burin yin zabe ajiye mukaminsu watanni shida kafin zaben. Sashen kuma da shugaban ya ce dole a gyara a matsayin sharadin amincewa da dokar da ke da jan aikin jagorantar zabe a badi: "Wannan tanadi ya gabatar da hanyar cancanta ko rashin ta, inda ta ci karo da kundin tsarin mulki ta hanyar haramtawa nadaddu na siyasa damar da kundin tsarin mulkin kasa ya tabbatar musu. Aiwatar da sashe na 84 karamin sashe na 12 na sabuwar dokar zaben, zai kai ga kwace damar masu rike da mukaman siyasar kamar yadda sashe na 40 da na 42 na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 ya tanadar."

Najeriya | Majalisar Dattawa | Abuja
Majalisar dokokin Najeriyar dai, ta jima da kwaskware dokar zabenHoto: Uwais Abubakar Idris/DW

Ana dai zargin masu yin dokar da sakaya tsarin da nufin toshe damar gwamnoni da shi kansa shugaban kasar, amfani da nadaddun wajen cika burikansu na siyasa. To sai dai kuma a fadar Aisha'tu Dukku da ke zaman shugabanr kwamitin zabe na majalisar, matakin nasu ba shi da wani laifi. Dokar dai kuma a fadar Sanata Ahmad Lawal da ke zaman shugaban majalisar dattawa ta kasar, na shirin sauya da dama a cikin fagen siyasar Najeriyar mai tsananin rikici. To sai dai koma wane tasiri dokar ke iya yi wajen kai wa ya zuwa ga tabbatar da ingantaccen zabe dai, ko bayan jami'ai na gwamnatin APC su kansu masu adawa ta kasar sun ce sun gamsu da kokari na kai wa ya zuwa ingantaccen zabe kamar yadda a fadar Sanata Yabagi Sani da ke zaman shugaban gamin gambizar jam'iyyu na kasar ya tabbatar. Da sabuwar dokar dai ana saran Hukumar Zabe mai Zaman Kanta ta Najeriyar INEC, za ta sanar da ranakun yin zaben da ma ragowar shirin mai tasiri a zuciyar 'yan kasa.