1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Koma bayan cinikin Afirka da Najeriya

June 30, 2023

An samu raguwar ciniki tsakanin Tarayyar Najeriya da ke zaman mafi yawan al'umma kana guda cikin mafiya karfin tattalin arziki a Afirka da ragowar kasashen nahiya.

https://p.dw.com/p/4THtP
Najeriya | Tattalin Arziki | Kasuwanci Mara Shinge
Ko akwai yiwuwar nan gaba Najeriya ta ci moriyar kasuwanci mara shinge?Hoto: Getty Images/AFP/S. Kambou

Cikin fatan habaka tattalin arziki da kila kai wa ya zuwa kare talauci ne dai, kasashen nahiyar Afirkan 54 suka rattaba hannu kan yarjejeniyar cinikin bai daya. To sai dai kuma shekaru uku bayan nan, har yanzu fatan na kama da mafarkin rana a Najeriya. Sannu a hankali dai ciniki na dada raguwa a tsakanin Najeriyar da ke fatan cin moriyar kasuwar mai tasiri da ba ta da shinge da kuma ragowar kasashen nahiyar da ke kallon dama, a yawan al'ummar da Najeriyar ke da su. Daga bara zawa shekarar bana dai, Najeriyar ta fuskanci raguwar huldar kasuwancin da ta kai kaso kimanin 11 cikin 100 na yawan kasuwancin da ta yi da kasashen nahiyar. A yayin da alal ga misali Abujar ta kalli cinikin da ya kai Naira miliyan dubu 950 a farkon watanni  uku na shekarar da ta shu de a tsakanin bangarorin biyu, a wattani uku na shekarar bana cinikin ya ragu ya zuwa Naira miliyan dubu 840. Tun bayan kaddamar da yarjejeniyar da ke da babban burin ciniki mara shinge dai,  Najeriyar ke kallon raguwar ciniki da kasashen Afirkan.

Ruwanda | Kigali | Afirka | Kasuwanci Mara Shinge
A shekara ta 2018 kasashen Afirkan suka amince da yin kasuwanci mara shinge a KigaliHoto: Getty Images/AFP/STR

Kuma ciniki a tsakanin bangarorin biyu ya ragu daga kaso 11 a shekara ta 2020 da aka kaddamar da kasuwar ya zuwa sama da kaso bakwai a shekara ta 2021, sannan kuma da sama da kaso shida a shekarar da ta shude. Mohammed Labaran dai na zaman shugaban kwamitin amintattu na masu kasuwar Najeiryar da kuma ya ce, ana da tambayar amsawa kan matakai na gwamnatin tarayya kan habaka ciniki cikin kasar. Ko bayan cin hanci da ma uwa uba rashin imani kan yarjejeniyar dai, tun can dai Najeriyar na zaman kasa ta karshe da ta amince da rattaba hannu a kan yarjejeniyar da ta kafa kasuwar bayan doguwar takkadama da ma kai kawo. Akwai dai tsoron baba-kere da kila ma jibge kayan Turawan da a kan sauyawa kwali kuma a nemi shigo da su zuwa Najeriyar, kasa mafi girman kasuwa a nahiyar baki daya. Dakta Isa Abdullahi dai na zaman kwararre ga batun tattalin arzikin Najeriyar, kuma ya ce manufofin gwamnatin kasar ba su bayar da damar habaka ciniki da kasashen nahiyar Afirkan ba.