Najeriya ta kama 'yan Poland da zargi a kan ɗaga tutar Rasha
August 8, 2024Wannan dai labari ne da hukumar bincike ta farin kaya a Najeriyar ta tabbatar, hukumar da ta kama har da wasu telolin da suka dinka tutar ta Rasha da gomman mutane suka yi ta ɗagawa a jihar Kano da ke arewacin kasar.
Shi ma babban jami'in jakadancin kasar Poland a Najeriya, Stanislaw Gulinski ya ba da labarin kame 'yan kasar tasa a lokacin wata ganawa da ministan harkokin wajen Najeriya a Abuja.
Dubban daruruwan 'yan Najeriya ne ke zanga-zanga tun a ranar daya ga wannan watan, saboda rashin jin dadi da yadda gwamnatin Shugaba Tinubu ke tafiyar da harkokin tattalin arziki.
Rayuwa dai ta yi wa miliyoyin 'yan Najeriyar tsauri musamman bayan janye tallafi a kan man fetir da na wutar lantarki da shugaban kasar ya yi.
Kungiyar kare hakkin bil Adama ta Amnesty Int'l ta ce mutane 22 suka mutu a zanga-zangar a yankin arewacin Najeriya.