1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

NATO: China na fadada makaman nukiliya

Abdul-raheem Hassan
September 6, 2021

Sakatare janar na kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg, ya bukaci kasar China ta shiga sahun sauran kasashen duniya da ke yunkurin hana yaduwar makaman nukiliya a duniya.

https://p.dw.com/p/3zzko
NATO Secretary General Jens Stoltenberg
Hoto: Francisco Seco/Pool/AP/picture alliance

Da yake bayyana muhimman batutuwa kan rage mallakamar makaman nukiliya a taron shekara-shekara na kungiyar tsaro ta NATO, Stoltenberg ya ce akwai bukatar tafiya tare da sauran manyan kasashen duniya don takaita yaduwar manyan makamai ba wai a tsaya kan takawa kasar Rasha kadai birki ba.

Sakatare janar na kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg ya ce "A halin yanzu, makaman nukiliya na kasar Sin yana fadada cikin hanzari. Haka kuma, kasar Sin tana gina adadi mai yawa na makamai masu linzami, wanda zai iya kara karfin nukiliyarta sosai. Duk wannan yana faruwa ba tare da takunkumi ba, kuma ana yin hakane ba tare adalci ba." inji Stoltenberg.