Kira ga 'yan siyasa a Nijar kan zabe
February 22, 2021Za dai a iya cewa wannan kiran nasu na zuwa ne ta la'akari da yadda aka fara gudanar da yakin neman zaben Jamhuriyar ta Nijar zagaye na biyu, inda har hukumomin suka yi ta yin kashedi ga 'yan kasar sakamakon kalaman da suka fara tasowa a wancan lokacin.
Karin Bayani: Dan takarar adawar Nijar, ya sa an soke muhawara
Kusan kowane lokaci idan aka kammala zaben, shugabanin 'yan siyasar na wata al'adar neman zaman lafiya wadda ko a yanzu akwai bukatar sake maimaita hakan bayan zaben, inji Hassan Bako na hadin gwiwar kungiyoyin farar hula CODDH. Galibin lokuta dai ana amfani da matasa wajan tayar da zaune tsaye, to amma Allassan Abubakar na wata kungiyar matasa TJDL, ya ce a nan Nijar dai ba za su bari ayi amfani da su domin cimma wata manufa ba.
Su ma dai 'yan siyasar a nasu bangaren, sun nuna a shirye suke su mutunta sakamakon. Haka abin yake a bangaren 'yan adawa, inda suma suka daga murya ga magoya bayansu da su bayar da kai bori ya hau ga sakamakon da zai biyo baya. Tun dai gabanin zaben ne malaman addinai ke amfani da wuraren ibada domin isar da sakonin zaman lafiya, duba da yanayin kasar.
Karin Bayani: An hana rantsuwa da Al-Qur'ani a Nijar
Yanzu haka dai hukumar zaben kasar CENI wadda ita kadai ce ke da hurumin bayar da sakamakon na ci gaba da wallafa shi sannu a hankali, inda bayananta ke nuni da cewa Bazoum Mohamed dan takarar jam'iyar PNDS Tarayya mai mulki ne ke da rinjaye a gaban Mahamane Ousmane na RDR CANJI, koda yake ana ci gaba da tattara sakamakon.