Nijar ta dage lokacin komawa makaranta sakamakon ambaliya
September 20, 2024Gwamnatin Nijar ta dage lokacin fara zangon karatu na bana daga 2 zuwa ranar 28 ga watan Oktoba sakamakon barnar da ambaliya ta yi a makarantu da dama tare da fuskantar mamaye ajujuwa daga wadanda ruwa ya raba da muhallansu. Tun dai watanni hudu da suka gabata ne, ruwan sama ke haddasa ambaliya a yankuna da dama na Nijar, lamarin da ya shafi makarantu da dama , a cewar sanarwar taron majalisar ministocin da aka karanta a gidan talabijin na kasar.
Karin bayani: Nijar: Malaman kwantaragi sun koka kan albashi
A yankin Maradi ne iftila'in ya fi barna, inda ka kafa tantuna kusan 100 don tsugunar da wadanda ambaliya ta sa su da fake a makarantu. Amma a Zinder ma, wani masallaci da aka gina sama da shekaru 200 da suka gabata ya ruguje sakamakon mamakon ruwan sama da aka yi a birnin.
Karin bayanNijar: Shirye-shiryen dakatar da amfani da ajujuwan zana a makarantun kananan yarai:
Kididdigar da ma'aikatar cikin gida ta Nijar ta fitar ta nunar da cewar ya zuwa ranar 4 ga watan Satumba, mutane 273 sun mutu yayin da aka samu rugujewar gidaje 152 sakamakon ambaliyar ruwa. Amma dai gwamnatin mulkin soja ta ce ta samar da fiye da tan 9,742 na hatsi ga yankuna takwas domin taimaka wa mutane miliyan daya da ambaliyar ruwa ta shafa. Jamhuriyar Nijar ta saba fuskantar ambaliya a lokutan damuna , ciki har da yankunan hamada na arewacin kasar inda aka sake samun gagarumar barna a bana.