1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Pakistan: Kotu ta bayar da belin Khan

Abdullahi Tanko Bala
December 22, 2023

Kotun kolin Pakistan ta bayar da belin tsohon Firaministan kasar Imran Khan a karar da ake tuhumarsa da fallasa sirrin gwamnati.

https://p.dw.com/p/4aUo2
Imran Khan
Hoto: Mohsin Raza/REUTERS

Kotun ta kuma bayar da belin mataimakin shugaban jam'iyyar Khan kuma tsohon ministan harkokin waje Shah Mahmood Qureshi.

Tsohon Firaministan na Pakistan dai kotu a baya ta yanke masa hukuncin daurin shekaru uku a gidan yari kan tuhumar cin hanci da rashawa.

An jingine hukuncin amma ya ci gaba da zama a tsare tun watan Augusta saboda wasu kararraki da ake tuhumarsada suka hada da baiyana sirrin kasa.

Daya daga cikin lauyoyin Khan Salman Safdar ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Reuters cewa babu tabbas ko da wannan hukuncin belin da kotun ta bayar za a bar Imran Khan ya fita daga gidan yari.