Paparoma ya yi kiran a kawo karshen yakin Syria
April 2, 2018Shugaban darikar Katholika na duniya Paparoma Francis, ya yi kiran kawo karshen zubar da jinin da ke ci gaba da wakana a kasar Syria da ma wasu kasashe na yankin gabas ta tsakiya. Paparoman ya yi wannan kiran ne a sakon bikin Easter na bana, yana mai jaddada kiran shugabanni su tabbatar da zaman lumana a fadin wannan duniya ta Allahu.
A sakonsa musamman ga shugabannin soji da na siyasa, jagoran mabiya darikar Katholikan ya nuna matukar bukatar dakatar da ta'asar da ke faruwa a Syria da yankin Gaza, jawabin da ya yi a gaban mabiya dubu 80 a dandalin St. Peters.
Yayin da Paparoman ke wannan kiran, wasu rahotannin na cewa an cimma yarjejeniyar da za ta bai wa fararen hula damar ficewa daga sauran wuraren da ke a gabashin Ghouta, inda ake fafata wuta a Syriar.