Paul Biya ya zarce kan mulkin Kamaru
October 22, 2018Shugaban dan shekaru 86 zai ci gaba da zama a karagar mulki har sai shekarar 2025 lokacin da zai kai shekaru 93 da haihuwa.
Shugaba Biya dai shi ya kwashe sama da kashi 70 cikin dari na kuri'u kana Maurice Kamto na jam'iyyar CRM shi ya zamo na biyu, sai kuma Cabral Libii na jam'iyyar Universe ya zamo na uku.
Gabanin bayyana sakamakon, sai da aka baza jami'an tsaro a manyan birane tare da haramta duk wani gangami da 'yan adawa ka iya yi a kasar.
Bayanai sun ce gabanin sanar da sakamakon, an ga wasu dakarun gwamnati a gidajen manyan 'yan takaran adawa, wadanda suka yi kiran 'yan Kamaru da su kare 'yancinsu, muddin sakamakon da aka bayyana ya ci karo da abin da suka zaba.
A share guda kuwa wasu bayanan na cewa an ji amon harbe-harbe a yankin kasar na renon Ingila da wasu ke neman ballewa.