1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Paul Biya: Za a ci gaba da murkushe masu neman ballewa

March 16, 2018

Gwamnatin kasar Kamaru, ta sha alwashin ci gaba da amfani da karfi na soji wajen murkushe 'yan bangaren nan da ke neman ballewa, a sashen kasar mai amfani da Ingilishi.

https://p.dw.com/p/2uQbd
Nordkamerun Grenzregion zu Nigeria Soldaten Anti Terror
Dakarun Kamaru cikin shirin kai farmakiHoto: AFP/Getty Images

Shugaba Paul Biya na kasar Kamaru, ya sha alwashin ci gaba da amfani da karin karfi na soji wajen ganin bayan 'yan bangaren nan da ke neman ballewa, a sashen kasar mai amfani da Ingilishi. A jiya ne dai shugaban na Kamaru ya sanar da hakan lokacin taron majalisar ministocin kasar karo na farko, bayan sama da shekaru biyu da zama irinsa.

Shugaba Biya ya ce dole ne a ci gaba da amfani da karfin na soji, don ganin an tabbatar da daidaito ta fuskar zamantakewa da kuma na arziki a yankin. Cikin watan Oktobar bara ne dai bangaren kasar da ke da karamin rinjaye, ya ayyana kafa kasar da ya kira jamhuriyar Ambazoniya, yankin da bai wuce kashi daya cikin biyar na yawan al'umar Kamarun ba.