1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Putin ya ce Rasha ta zama gagarabadau

Abdullahi Tanko Bala
May 9, 2020

Kasashen Rasha da Ukraine sun gudanar da tuni da zagayowar ranar da aka kawo karshen yakin duniya na biyu ta hanyoyi mabanbanta.

https://p.dw.com/p/3byij
Russland Moskau Wladimir Putin Gedenktag Tag der Befreiung Zweiter Weltkrieg Rede
Hoto: Reuters/A. Druzhinin

Rasha ta gudanar da bikin samun nasara akan sojojin Nazi na Jamus a lokacin yakin duniya na biyu, sai dai barkewar annobar corona ta sa an takaita hidimomin da aka tsara wadanda ake gani za su kambama goyon baya ga shugaba Vladimir Putin.

Shekaru 75 da suka wuce, Rasha da Ukraine da sauran sojojin tarayyar soviet suka afkawa Jamus sai dai har yanzu an kasa gudanar da bikin hadin gwiwa na bai daya a tsakanin kasashen domin tuni da muhimmiyar ranar.

A jawabinsa shugaba Putin ya jinjinawa sojojin kasar da suka kwanta dama. 

"Yace sojojinmu sun yi yaki ta sadaukar da rayuwa kuma ba za mu manta da wannan bajinta da suka nuna ba. Kanmu a hade yake wajen nuna jimami tare da daukar alhakin abin da ya wanzu a baya da kuma makoma ta gaba. Mun yarda mun yi amanna ba za a yi galaba akan mu ba."